Gwamnonin Najeriya 11 sun kai ziyara matatan Dangote da ake gina wa (Hotuna)

Gwamnonin Najeriya 11 sun kai ziyara matatan Dangote da ake gina wa (Hotuna)

- Mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a ranar Juma'a 20 ga watan Disamba sun ziyarci matatan man fetur na Dangote da ke Legas

- Shugaban kungiyar, gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya jagoranci tawagar gwamnonin

- Fayemi ya bayyana matatar ta Dangote a matsayin abin alfahari ga nahiyar Afrika

Gwamnonin jihohin Najeriya 11 a jiya Juma'a, 20 ga watan Disambar 2019 sun ziyarci Matatan Man Fetur na Dangote da ke Lekki a jihar Legas domin duba yadda aikin ke tafiya.

Gwamnonin sun hada da Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa), Okezie Ikpeazu (Abia), Mallam Nasir El-Rufai (Kaduna), AbdulRahman AbdulRasaq (Kwara), Prince Dapo Abiodun (Ogun), Godwin Obaseki (Edo), Dr. Kayode Fayemi (Ekiti), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Babagana Zulum (Borno), Simon Lalong (Plateau) da Bala Muhammed (Bauchi), yayin da mataimakan gwamnan jihar Cross Rivers, Ivara Esu, ya wakilci gwamnan jihar Benedict Ayade.

Gwamnonin wanda shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya NGF, Dakta Fayemi Kayode ya jagoranta sun bayyana matatan man na Dangote a matsayin abin alfahari a Najeriya da Afirka wadda zai taimaka sosai wurin habbaka tattalin arziki da samar da abinci a kasar da zarar ya fara aiki.

DUBA WANNAN: Kotu ta ci tarar jami'an tsaron da suka cafke karuwai a Abuja

Gwamnonin Najeriya 11 sun kai ziyara matatan Dangote da ake gina wa (Hotuna)
Gwamnonin Najeriya 11 sun kai ziyara matatan Dangote da ake gina wa (Hotuna)
Asali: Twitter

Gwamnonin Najeriya 11 sun kai ziyara matatan Dangote da ake gina wa (Hotuna)
Gwamnonin Najeriya 11 sun kai ziyara matatan Dangote da ake gina wa (Hotuna)
Asali: Twitter

Ya ce, "wannan muhimmin aiki ne da shugaban kamfanin Dangote, Mista Aliko Dangote ya fara. Hakan na nuna irin yadda 'yan Najeriya za su iya aikata abubuwan da zai kai kasar ga nasara idan gwamnati ta ba su dama kamar yadda gwamnatin jihar Legas ta yi.

"Hakan ya bashi damar fara wannan katafaren aiki ta naira biliyan 12 da an kusa kammalawa kuma saboda girmansa dole muka dakata kafin mu gama zagawa domin mu samu damar zuwa yin wasu ayyukan.

"Wannan abin alfahari ne ga Afirka ba Najeriya kadai ba. Ban san kasar da ke da irin wannan matatan ba a Afirka. Bana tsamanin ko a duniya akwai wurare masu kama da wannan da yawa, mun ji dadin damar da aka bamu na ganin ayyukan.

"Muna fatan ganin abubuwan da za a rika sarrafawa daga wannan kamfanin. Kamar robobi, man fetur da takin zamani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel