Gobara ta tashi a kasuwar wayoyi a Bauchi

Gobara ta tashi a kasuwar wayoyi a Bauchi

Gobara ta kone shaguna da dama inda aka yi asarar dukiyoyin miliyoyin naira a kasuwar sayar da wayoyin salula da aka fi sani da 'Kwantena' a kasuwar Wunti a garin Bauchi.

Wani mai gadi a kasuwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce gobaran ta fara ne misalin karfe 12 na dare kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gobarar da ake zargin wutan lantarki ne ya yi sanadin tashin ta ta kona shaguna 12.

Gwamnan jihar, Sanata Bala Muhammed ya ziyarci inda abin ya faru kuma ya yi wa 'yan kasuwan jaje inda ya ce su dauki abinda ya faru a matsayin kadara daga Allah.

DUBA WANNNAN: Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya karba nadin da Ganduje yayi masa

Gwamnan da mataimakinsa Sanata Baba Tela ya wakilta ya umurci hukumar bayar da taimakon gaggawa ta jihar ta tallafawa wadanda abin ya shafa inda ya kara da cewa gwamnati za ta dauki matakin kawo karshen afkuwar yawaitar gobara a jihar.

A yayin da ya ke jawabi, shugaban kungiyar 'yan kasuwan Wunti, Malam Iliyasu Muhu ya mika godiyarsa ga gwamnan bisa ziyarar da ya kai musu kuma ya yi kira da gwamnati ta tallafawa wadanda abin ya shafa domin su samu jarin da za su cigaba da kasuwancin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel