Idan na fallasa abinda ke faruwa a Najeriya, babu wanda zai iya bacci - TY Danjuma

Idan na fallasa abinda ke faruwa a Najeriya, babu wanda zai iya bacci - TY Danjuma

Tsohon ministan tsaro, Janar TY Danjuma, ya ce idan ya fallasa abubuwan da ke faruwa a kasar nan, yan Najeriya ba zasu iya bacci ba.

Tsohon Sojan ya bayyana hakan a wani taron karrama wasu da lambar yabo da kaddamar da littafi kan shekaru 70 da aikin jarida na jaridar Tribune, da ya gudana a jami'ar Ibadan, jihar Oyo.

Yace: "A kasar Yarabawa, kowa ya zama zabo, matsorata. Kuma da alamun mutane basu damu da abinda ke faruwa ba. Idan na fada muku abinda ke faruwa a Najeriya a yau, ba zaku iya bacci ba.

"Muna cikin halin dar-dar a kasar nan. Kuma mutanen da suka sanyamu cikin wannan hali sun cigaba a yau. Saboda haka ya kamata mu tashi tsaye. Shine hanya daya na tsirar da kawunanmu."

"Abubuwan da Yan jaridar bogi keyi ba ya taimakonmu. Muna rokon Ubangiji ya cigaba yiwa kasar nan albarka, amma mu kadai zamu iya ceton kanmu."

DUBA NAN: Shugaba Buhari ya kaddamar sabbin motocin yan sanda 217

A wani labarin daban, asu gungun miyagu yan bindiga guda ne suka kashe jagoransu bayan sun kama shi satar kudin da suka sato dumu dumu.

Jaridar Information Nigeria ta ruwaito yan bindigan da aka bayyana sunayensu kamar haka; Iweh Kevwe da Emmanuel Ogibi sun kama jagoransu Raymond Enahon ne inda suka daure shi tamau, suka jefar da shi a cikin dajin Obiaruku a jahar Delta, har ya mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel