Zina yake da kanwata shine ma abinda yasa ya gyara musu gidansu - Budurwa ta tonawa Fasto asiri

Zina yake da kanwata shine ma abinda yasa ya gyara musu gidansu - Budurwa ta tonawa Fasto asiri

- Wata budurwa mai suna Scilla ta caccaki Fasto Johnson Sulaiman a kafar sada zumuntar tuwita

- Ta zargi faston da lalata da ‘yar uwarta don kuwa har gyara gidan iyayenta yayi don faranta mata

- Ta caccakeshi ne bayan da yake wa’azi a kan Kirista nagari a shafinsa na tuwita

Wata budurwa mai suna Scilla_xx a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita, ta kalubalanci babban faston Omega Outreach Christian Ministry mai suna Apostle Johnson Suleman, a kan kwanciya da ‘yar uwarta kuma yana wa’azin a zama Kiristoci nagari.

Kamar yadda budurwar ta ce, Apostle Suleiman yana kwanciya da ‘yar uwarta, kuma ya gyara musu gidansu dake Auchi, jihar Edo don ya sanya ta farin ciki.

Scilla ta bayyana hakan ne a yayin da take mayar da martani a kan wa’azin da malamin addinin Kiristan yake yi a shafinshi na tuwita. Ya bukaci duk ‘Kiristoci nagari’ da su goge manhajar Netflix daga wayoyinsu sakamakon fim din batanci ga Yesu da kamfanin ya saki.

KU KARANTA: Amfanin ridi 13 a jikin dan adam da ba kowane ya sani ba

Ta kalubalanci yadda malamin yake maganar ‘Kiristoci nagari’ bayan da yake kwanciya da ‘yar uwarta.

Faston ya wallafa: “Ku goge manhajar Netflix daga wayoyinku. Ku dena binsu idan har kun kasance kiristoci nagari. Fim dan ‘Luwadin Yesu’ cin zarafi ne ga addinin Kirista. Mun kushe shi kuma bamu sonshi. Mahaukatan mutane…”

Scilla ta bada amsa kamar haka: “Kana ta lalata da ‘yar uwata. Ka gyara gidansu dake Auchi don ka faranta mata rai. Yanzu kuma kwatsa kana zancen “Kirista nagari”?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel