Bayan shekaru 150: Tattaba kunne sun garzaya kotu don karbar gado

Bayan shekaru 150: Tattaba kunne sun garzaya kotu don karbar gado

Wasu tattaba kunne a jihar Kano sun garzaya gaban wata kotun majistare dake Dorayi don bukatar gadonsu. Ba bukatar gadon bace abun mamaki, sun bukaci alkali ya fitar musu da hakkinsu a kan wani fili da mahaifin kakansu, marigayi Alhaji Garba ya bayar a wani lokaci.

Marigayi Alhaji Garba ya bada filin ne don a gina makabarta a wancan lokacin da ya shude.

Wannan lamarin ya faru ne a unguwar Dorayi dake karamar hukumar Gwale. Magadan sun fahimci cewa suna da nasu kason a cikin wannan yankin na makabarta.

Kamar yadda magadan suka bayyana, wasu masu hannu da shuni ne suka nuna halin ko-in kula a kan makabartar da gidajensu ke jiki.

Sun bayyana cewa, mutanen da suka dinga cin iyakar makabartar sun hada da Marigayi Alhaji Uba Safiyanu, Alhaji Sabo da Alhaji Mamuda.

Wakilin gidan rediyon Freedom ya tattauna da masu makwabtaka da wannan makabartar don jin ta bakinsu a kan gaskiyar lamarin.

DUBA WANNAN: Osinbajo ya jagoranci zaman NEC na karshe a shekarar 2019

Wani mazaunin unguwar mai suna Dahiru Isa, yana daga cikin wadanda suka ga mika takardar sammaci daga kotun zuwa mai unguwar Dorayi, kuma suka jagoranci zagaye makabartar.

Kamar yadda kotun ta ce, mai unguwa ya raina kurar kotun don bai halarci zamanta ba. Amma lauyansa yace ba hakan bane, don Mai Unguwa bai samu takardar sammacin bane.

Dahiru Isa ya ce, tuni kotu ta aike da sammaci ga wadanda ake zargi da hannunsu cikin badakalar. Sun hada da Nafi'u, Shfi'u da kuma mai Unguwar sashin yaki da daba na rundunar 'yan sanda reshen jihar Kano.

Hakazalika, wasu daga cikin 'yan unguwar sun bukaci alkalin da ya sauya wajen gudanar da wannan shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel