Na samu wasika daga kungiyoyin Kano 35 na bukatar sauke Sarkin Kano - Ganduje

Na samu wasika daga kungiyoyin Kano 35 na bukatar sauke Sarkin Kano - Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Alhamis ya bayyana cewa ya samu wasika daga kungiyoyin fafufutuka 35 inda suka bukaci ya kwancewa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, rawani kan rashin biyayya.

Mai magana da yawun Ganduje, Abba Anwar, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki inda ya bayyana cewa kungiyoyin sun nuna damuwarsu kan yadda sarkin ke kokarin kafa wata jihar cikin jihar Kano.

Abba Anwar bai lissafa sunayen kungiyoyin ba amma ya ce shugabansu Ibrahim Ali, ya rattafa hannu kan wasikar.

Tun bayan zaben 2019, gwamna Ganduje ya rage karfin Sarki Sanusi ta hanyar kirkiro sabbin masarautu hudu masu matsayi na daya.

Ganduje ya bayyana cewa mutan jihar Kano ne suka bukaci kafa wadannan sabbin masarautun kuma suna farin ciki da hakan.

Amma masu sharhi kan lamuran yau da kullum da kuma abokan hamayyar gwamnan sun bayyana cewa ana yiwa Sarkin bita da kulli ne saboda adawar da ya nunawa gwamnan a zaben 2019.

A jawabin, Anwar bai fayyace ko gwamnan zai kadddamar da bukatar kungiyoyin ba kuma bai fadi lokacin da zai yi ba.

KU KARANTA: Kan satan Kaji, kotu ta yankewa Yusuf Musa hukuncin shekarar 1 a Kurkuku

A bangare guda, karo na farko tun bayan kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano, sabbin sarakunan da aka nada sun share junansu a wurin taron da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya halarta a karamar hukumar Wudil ranar Alhamis.

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi bakuncin shugaba Buhari yayin ziyarar da ya kai Kano domin halartar bikin yaye wasu dalibai da suka kammala karatu da karbar horo a jami'ar 'yan sanda dake Wudil.

Kafin wannan taro na ranar Alhamis, sabbin sarakunan basu taba haduwa da juna ba tunda gwamna Ganduje ya keta masarautar Kano zuwa gida biyar, kowacce da sarkinta na yanka mai cikakken iko.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel