Kan satan Kaji, kotu ta yankewa Yusuf Musa hukuncin shekarar 1 a Kurkuku

Kan satan Kaji, kotu ta yankewa Yusuf Musa hukuncin shekarar 1 a Kurkuku

Wata kotu dake zamanta a Kasuwan Nama, birnin Jos a ranar Alhamis, ya yankewa wani matashi dan shekara 22, Yusuf Musa, hukuncin daurin shekara daya a gidan gyara hali.

Alkali mai shari'a, Yahaya Mohammed, ya jefa Musa gidan yari bayan ya amsa laifin satan Zakara.

Amma daga baya, Alkalin ya bashi daman biyan tarar N10,000 domin ceton kansa.

Alkalin ya ce wannan zai zama darasi ga wadanda ke sha'awar aikata irin wannan laifi.

Lauyan hukumar, Ibrahim Gokwat, ya laburtawa kotu cewa an kai kararsa ofishin yan sandan Laranto.

Lauyan ya ce mai kiwon kajin ya ji kukansu ne sai ya fita dubasu kawai yayi arangama da barayin biyu da kaji a hannunsu.

"Da Mai kajin ya yi ihu barawo, sai suka ajiye kajin suka arce amma makwabta suka kure musu gudu har suka damke daya daga cikinsu." Yace

DUBA NAN Watan Junairu za'a fara layin dogon Ibadan zuwa Kano - Amaechi

A wani labarin daban, Wata babbar kotun Abuja dake zamanta a garin Zuba ya yanke hukuncin bulala goma sha biyu ga wani mutumi mai suna Yakubu Nasiru da aka kama da satar burodi, kwai da man bota.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa Alkalin kotun da ya yanke wannan hukunci, Gambo Garba ya gargadi Yakubu Nasiru daga aikata irin wannan laifi a nan gaba, sa’annan ya shawarce shi ya nemi sana’ar yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel