Gwamnati za ta siya 'Keken a daidaita sahu' 3 a kudi N40m

Gwamnati za ta siya 'Keken a daidaita sahu' 3 a kudi N40m

Ma'aikatar kiwon lafiyan tarayya za ta kashe milyan arba'in wajen siyan keken a daidaita sahu na daukan marasa lafiyan gaggawa ga wani asibiti a jihar Benue.

A cikin lissafin kasafin kudin 2020, N40m aka ware na siyan babura masu kafa uku wanda akafi sani da 'Keke Napep' ko a daidaita sahu guda uku ga asibitin Odessessa PHC dake Okpokwu, jihar Benue.

Hakazalika, ma'aikatar ta yi kasafin cewa za tayi amfani da N230million wajen gyara da sayen kayayyakin asibiti da magunguna ga asibitocin PHC dake yankunan tarayya shida.

Amma, ba'a bayyana ainihin wuraren da za'a gyara ba kuma babu bayanin inda za'a kai magungunan.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa rashin sanya wuraren da za'a kai wadannan kayayyaki matsala ne saboda ba za'a iya bibiyan ayyukan ba.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya shilla jihar Kano

Hakazalika, yan Najeriya sun yi ca kan ware bilyan 37 domin gyaran majalisar dokokin tarayya.

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta soki wannan kudi da za a batar, inda ta ce kashe biliyan 37 wajen gyara ginin da aka yi a kan Naira biliyan 7 ya nuna cewa sata kurum APC ta nufa a fili.

A wani bincike da Jaridar Daily Trust ta yi, ta gano cewa za a iya amfani da wannan kudi wajen yin wasu aikace-aikacen da su ka fi yi wa majalisar kasar kwaskwarimar da zai amfani tsirarru.

Abubuwan sune Gina dakunan karatu 10, 000, Gidajen zama 12, 000, Dakunan shan magani 27, 000, Inganta Jami’o’i 37, Taimakawa ‘Yan kasuwa 1, 000, 000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel