Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban DPR

Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban DPR

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sarki Auwalu a matsayin shugaban hukumar da ke kula da man fetur ta kasa (DPR).

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya fitar da sanarwar nadin da Mista Auwalu.

Mista Adesina ya ce sabon shugaban da aka nada zai rike mukamin ne na tsawo shekaru hudu.

"Mista Auwalu wanda injiniya ne na sinadaren chemical ya kasance daya daga cikin jigo a hukumar ta DPR tun da ya fara aiki a hukumar a matsayin babban injiniya a 1998.

DUBA WANNAN: Yadda wasu mata biyu suka bawa hammata iska a bainar jama'a kan na miji

"Sabon direktan ya yi digirinsa ta farko ne a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuma ya yi dirgiri na biyu a Jami'ar Bayero ta Kano da PETRAD a kasar Norway da PetroSkill a kasar Amurka da ma wasu makarantun.

"Auwalu na cikin mambobin cibiyar injiniyoyi na sinadaran chemical na kasar Ingila, kuma mamba ne ne Kungiyan Injiniyoyin man fetur, da Kungiyar Injiniyoyi na Najeriya da kuma cibiyar injiniyoyi masu rajista ta Najeriya (COREN)."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel