Da Babangida bai yiwa Buhari juyin mulki ba, da Najeriya ta fi haka cigaba - Femi Adesina

Da Babangida bai yiwa Buhari juyin mulki ba, da Najeriya ta fi haka cigaba - Femi Adesina

Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya ce da maigidansa ya dade a mulkin soja da yayi a 1983, da Najeriya ta fi haka cigaba.

Adesina ya bayyana hakan ne a dogon jawabin da ya saki domin murnan cikar Buhari shekaru 77 a duniya ranar Talata.

Buhari ya jagoranci Najeriya a matsayin Soja tsakanin shekarar 1983 da 1985 da Ibrahim Babangida yayi masa juyin mulki.

A cewarsa, gwamnatin Buhari a lokacin na tafiyar da kasar yadda ya kamata kafin wasu yan kama karya suka kwace gwamnatin kuma suka mayar da hannun agogo baya.

KU DUBA: Matasa sun bankawa coci wuta kan zargin Fasto ya birne yaro ciki

Yace: "Na fada kuma ina maimaitawa. Na dade ina bibiyar Buhari tun yana shugaban kasan mulkin Soja, lokacin da nike karatu a jami'a."

"Kuma da mulkinsa ta dade, Najeriya ba zata kasance cikin halin kakanikayen da take ciki yanzu ba. Mulkinsa na da zafi, amma tana tafiyar damu hanyar shiriya."

"Baku san yadda nayi farin ciki lokacin da Buhari ya zama shugaban kasar demokradiyya bayan shekaru 12 yana gwagwarmaya ba. Ban taba tunanin za'a dama dani cikin mulkin ba, amma na smau kaina ciki."

"Sabanin shugabannin da suka shude, Buhari ba barawo bane. Mun san mutanen da dubunnai kawai suka mallaka lokacin da suka hau mulki a kasar nan, amma suka fito da mahaukatan kudi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel