To fah: Yadda wata karuwa ta shiryar dani ta gyara mini rayuwata - Wani mutumi

To fah: Yadda wata karuwa ta shiryar dani ta gyara mini rayuwata - Wani mutumi

- Wani dan Najeriya ya bayyana labarin rayuwarshi ta yadda akalarta ya sauya

- Ya bayyana yadda karuwa ta sauya mishi rayuwa kwata-kwata

- Ya rainata a matsayin karuwa, amma ashe arzikinsu na tare da ita, ta hanyarta suka samu kwangilar da ta canza musu rayuwa

Wani dan Najeriya ya bayyana labarin rayuwarshi ta yadda karuwa ta sauya akalarshi. Ya aminta da cewa, darasin da ya koya zai amfani mutane da yawa. Abubuwa masu kyau na iya zuwa daga inda ba a tsammani.

"Makonnin da suka gabata, naje wani taron yara a Fatakwal. Taron ya samu halartar manyan mutane har da kwamishina a taron. Taron na yaron wani abokina ne na yarinta.

"Bayan kammala karatunmu a jami'a, sai muka bar kauye muka dawo Fatakwal mu uku inda muka kama daki daya. Abinda muka fi bukata a lokacin shine: ci, sha, sutura, kudin haya da mata don rage zafi. A saboda haka ne muke zuwa mashaya don samun mace da zamu je da ita gida mu sasanta.

"A haka watarana abokina ya dauko karuwa ya kai gida. Amma karuwar nan ba irin kowacce bace. Don taki amincewa da mu, sai abokina shi kadai. Har fada sukayi dashi saboda mun kwana a dakin ranar da ya daukota.

KU KARANTA: Ku daina tsaface-tsaface da shiga kungiyoyin asiri - Limamin coci ya shawarci 'yan siyasa

"Daga nan kawai muka ga ya makale mata. Mun yi ta zargin mallakeshi tayi. Mun bashi shawara amma kwata-kwata ya ki saurararmu don kuwa soyayya suka fara da ita.

"Duk da bamu taba tozarta ta a kan idonta ba, mukan kusheta idan daga mu sai shi. Watarana sai karuwar abokina ta samo mana kwangila, kamar wasa. Babu dadewa hanyoyin arziki da alheri suka dinga bude mana ta hanyarta. Kamar almara muka canza gida kuma aka saka musu rana.

"Bayan aurensu duk mun siya motoci kuma kudi ya fara zauna mana. A takaice dai, a halin yanzu abokina ya zama babban mai hannu da shuni kuma barin kasar zasu yi da matarshi. Sun samu wata kwangila mai tsoka a Australia tare da matarshi wacce a da muka raina."

"A don haka ba zan raina karuwa ba don ta sauya akalar rayuwata kwata-kwata." In ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel