Yadda wasu mata biyu suka bawa hammata iska a bainar jama'a kan na miji

Yadda wasu mata biyu suka bawa hammata iska a bainar jama'a kan na miji

'Yan sandan kasar Kenya sun gurfanar da wasu mata biyu kan laifin gwabza fada a bainar al'umma kan wani mutum.

Sarah Wamaitha ta kama Mercy Murithi da fada ne a ranar 4 ga watan Nuwamba saboda tana kusantar mijinta ta hanyoyin da ba su da ce ba.

Ana tuhumar matan biyu da ke da shaguna a Sheikh Karume road a garin Nairobi da laifin tayar da hankulan al'umma ta hanyar gwabza fada a bainar jama'a.

An shaidawa kotun Makadara cewa mijin Wamaitha ya fada mata cewa Murithi tana kusantarsa tare da neman su aikata zina wadda hakan bai kwanta masa a rai ba.

Wani dan leken asiri da Wamaitha da dauka haya don ya tabbatar mata da zargin ya tabbatar wa kotu cewa hakan ya faru wadda hakan ya janyo fada a shagon sayar da waya na Murithi inda aka ce ta lalata waya.

DUBA WANNAN: Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi (Hotuna)

Daga bisani an kama matan biyu kuma aka tuhumarsu da tare bayan sun kai rahoto a ofishin 'yan sanda na Kamukunji a lokuta daban-daban.

Dukkansu biyu sun musanta aikata laifin da ake tuhumarsu da aikatawa. An sake su kan belin Ksh30 kowannensu.

Kotu ta dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 15 ga watan Afrilun 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel