Wa'iyazubillah: An kama wani yana zina da gawa a gaban abokinsa

Wa'iyazubillah: An kama wani yana zina da gawa a gaban abokinsa

Wani kwararren mai binciken sababin mutuwar mutane da dan dan sanda ya kama yana zina da gawa don murnar nasarar cin wasar kwallo da kungiyarsa ta yi ya rasa aikinsa.

Wanderley dos Santos Silva, mai shekaru 52 ma'aikacin Institute of Legal Medicine da ke Manus a Brazil ya yi kokarin tserewa bayan da dan sanda ya shigo dakin ajiyar gawar ya kama shi yana lalata da gawa a gaban abokin aikinsa kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

Dan sandan ya shiga dakin gawar ne don neman wani bayani kan gawar inda ya tarar da mutumin yana aikata wannan mummunan aikin tare da gawar wata yarinya.

An kori Silva da abokin aikinsa nan take kuma an shigar da kara zuwa ofishin 'yan sanda.

Tuni dai an fara bincike kan laifin na lalata da gawa. Duk da cewa ba a tabbatar ko an kama Silva ba, akwai yiwuwar za a yanke masa hukuncin zama gidan yari na shekara daya zuwa uku idan aka tabbatar da laifin.

DUBA WANNAN: Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi (Hotuna)

Sanarwar ta wata kafar yada labarai na kasar ta fitar ya ce:

"Sashin binciken kimiyya na 'yan sanda ta fara bincike kan rahoton da aka shigar na aikata zina da gawa da wani ma'aikacin binciken gawa ya aikata. An fara bincike kan rahoton a halin yanzu.

"An sallami ma'aikacin binciken gawar nan take tare da wani ma'aikaci.

"Jami'in dan sanda ne ya kama wanda ake zargin a dakin binciken gano sanadin mutuwar gawar.

"Abokan aikinsa sun ce an kama shi na yayin da ya ke saka wandonsa bayan ya sako daga teburin da gawar macen ya ke."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel