Kotu ta daure malamin jami'a a Kano saboda kunduma ashariya

Kotu ta daure malamin jami'a a Kano saboda kunduma ashariya

- Wata kotun majistare a jihar Kano ta bada umarnin garkame wani malamin jami'a a gidan maza

- Hakan kuwa ya biyo bayan kamashi dumu-dumu da ta yi da laifin kutuntuma ashariya ga wani

- A bukatar belin da lauyan malamin ya mika, kotun tace zata duba hakan nan da 19 ga watan Disamba

Wata kotun majistare da ke zama a Rijiyar Zaki ta aika wani malamin jami'a zuwa gidan gyaran hali bisa ga zarginsa da bata suna tare da cin mutunci.

Tun farko dai, 'yan sanda sun gurfanar da wannan lakcara mai suna Mustafa Hashim Kurfi, wanda wani mai suna Abba Musa ya kai korafi.

A korafin da Abba Musa ya mika, ya bayyana cewa Lakcaran ya duddura masa ashar tare da 'yan uwansa ta wayar tarho. Abba ya nadi muryar malamin yana ta kunduma musu ashar. Amma Malam Mustafa Hashim Kurfi ya musanta aukuwar lamarin.

DUBA WANNAN: Kunne ya girmi kaka: Alakar sarautar 'Sarkin Bai' da jihadin Shehu bin Fodio

Barista Ma'aruf Muhammad Yakasai shi ne lauyan da yake kare Mustafa Hashim. Ya kuma roko kotun da ta sanya shi a hannun beli kasancewar akwai dangatakar auratayya da ta hada wanda ake kara da wanda ya kawo karar.

Sai dai, dan sanda mai gabatar da kara ya soki hakan. Ya tabbatar da cewa, daga an bada belin Mustafa, toh akwai yuwuwar haifar da tarnaki wanda zai iya zama babbar barazana ga binciken jami'an 'yan sandan.

Mai Shari'a Aminu Usman Fagge ya sanya ranar 19 ga watan Disamba don bayyana matsayar kotun. ya kuma bada umarnin a cigaba da tsare wanda ake karar a gidan gyaran hali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel