Jam'iyyar APC ta yi ta'aziyar rasuwar tsohon mataimakin shugabanta na kasa

Jam'iyyar APC ta yi ta'aziyar rasuwar tsohon mataimakin shugabanta na kasa

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta bayyana bakin ciki bisa rasuwar tsohon mataimakin ta na kasa (yankin Arewa ta tsakiya), Alhaji Abdullahi Idde da ya rasu sakamakon mummunan hadarin mota.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Malam Lanre Issa-Onilu, cikin sanarwar ta ya fitar a babban birnin tarayya Abuja ya ce an yi wa mammacin addu'a yayin taron masu gudanarwa na jam'iyyar (NWC) da aka gudanar a jiya.

DUBA WANNAN: Gwamnonin PDP biyu sun yi cacar baki a kan Buhari

Issa-Onilu ya ce kwamitin masu gudanarwan ta tura tawaga ta musamman zuwa gidan tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa don isar da sakon ta'aziyya su.

Jam'iyyar da ta aike da sakon ta'aziyyar ta ga iyalan mammacin da gwamnati da al'ummar jihar Nasarawa ta yi addu'an Allah ya jikan marigayi Zakari Idde wanda kafin rasuwarsa shine shugaban kwamitin masu bayar da shawarwari na Lower Niger River Basin Development Authority.

Sunyi addu'ar Allah ya saka masa da gidan aljanna Firdausi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel