Yadda 'dan maina ya cire N58m daga bankin UBA - EFCC

Yadda 'dan maina ya cire N58m daga bankin UBA - EFCC

A ranar Litinin, Wani jami'in hukumar hana almundhana da yiwa tattalin arzikin zagon kasa EFCC, Mohammed Goji, ya bayyanawa kotu cewa Faisal Maina, yaron tsohon shugaban kwamitin gyara harkar fansho, Abdulrashid Maina, ya cire N58m daga cikin asusun kudi a bankin UBA.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Goji, wanda babban jami'in bincike ne a hukumar EFCC ya yi shaida a kotu inda ake gurfanar da Faisal Maina.

Goji ya bayyana hakan ne gaban Alkali Okon Abang, na babbar kotun tarayya Abuja.

Ya laburtawa kotu cewa Faisal ya cire kudi N58,101,585 daga asusun banki mai suna Alhaji Abdullahi Faisal Farm 2 da lamba 1018636805.

A makon da ya gabata, Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya bada umurnin mayar da shi kurkuku bisa ga bukatar lauyan Faisal, Mohammed Munguno, wanda ya bukaci kotun ta mayar da shi gidan gyara halin Kuje.

An gurfanar da Faisal ne ranar 25 ga watan Oktoba kan zargin aikata laifuka uku na safarar kudade, da zamba.

A ranar 26 ga Nuwamba, Alkali mai shari'a, Jastis Okon Abang, ya baiwa Faisal beli kan farashin milyan sittin da kuma mai tsaya masa.

Jastis Abanga ya bayyana cewa wajibi ne wanda zai tsaya masa ya kasance dan majalisan wakilan tarayya kuma ya kasance ya mallaki dukiya a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel