Kano: Sarkin Karaye ya sauke manyan hakimai guda 2 a karkashin masarautarsa

Kano: Sarkin Karaye ya sauke manyan hakimai guda 2 a karkashin masarautarsa

- Majalisar masarautar Karaye ta kwace rawunan hakiman Kiru da Rimin-Gado na yankin

- Hakan ya biyo bayan zargar hakiman da aka yi da laifin rashin biyayya da cin amana

- Tuni masarautar ta zabi wasu hakiman don maye gurbin wadanda ta sauke

Majalisar masarautar Karaye ta jihar Kano ta kwace rawunan hikimin Kiru, Alhaji Ibrahim Hamza da na hakimin Rimin-Gado, Alhaji Shehu Muhammad a kan zarginsu da take da cin amana.

Majalisar masarautar ta yanke wannan hukuncin ne bayan zamanta na biyo wanda ya samu shugabanci Sarkin Karaye, Dr. Ibrahim Abubakar II a fadar masarautarsa da ke Karaye.

Wannan na kunshe ne a takardar da jami’in yada labarai na masarautar Karaye, Alhaji Haruna Gunduwawa ya fitar a ranar Lahadi a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Asibiti: 'Yan fashi da makami sun yi wa majinyata da ma'aikatan asibiti fashi

“Majalisar masarautar ta amince da nada Alhaji Auwalu Ahmad a matsayin hakimin Rimin-Gado, Magajin Rafin Karaye, a matsayin hakimin Kiru da kuma Alhaji Garba Alhaji a matsayin Dan Madamin Karaye,” in ji shi.

Gunduwawa ya ce, majalisar ta amince da nadin Malam Shehu Ahmed a matsayin hakimin Karaye.

“Majalisar tana taya sabbin hakiman murna tare da musu addu’ar Allah ya sha gabansu a yayin sauke nauyinsu. Taron ya samu halartar shuwagabannin kananan hukumomin da ke karkashin masarautar da sauran ‘yan majalisar.” Cewar Gunduwawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel