Yadda Zulum ya fasa kwan yunkurin da El-Rufa'i, Bagudu da Badaru keyi na tsige Oshiomole

Yadda Zulum ya fasa kwan yunkurin da El-Rufa'i, Bagudu da Badaru keyi na tsige Oshiomole

Sabanin abinda suka sanar da sauran gwamnonin cewa za'a zo ganawa da shugaba Buhari, ashe gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i; gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da gwamnan jihar Jigawa, Badaru Talamiz; na shirya wani tuggu.

Wadannan gwamnoni sun shirya amfani da sauran gwamnonin da ke halarce a ganawar ne wajen tsige shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomole. The Nation ta ruwaito

Ana fara taro, gwamna El-Rufa'i ya bayyanawa shugaba Buhari cewa gwamnonin APC sun yanke shawarar cire Oshiomole saboda bai gudanar da jam'iyyar yadda ya kamata. Yace saboda haka suka zo sanar da shugaban kasa shirin da sukeyi.

Kawai sai gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya fasa kwan yunkurin da sukeyi inda ya laburtawa shugaba Muhammadu Buhari cewa El-Rufai, Fayemi, Bagudu da Badaru, na son kwace akalan jam'iyyar ne saboda daya daga cikinsu ya zama shugaban kasa a 2023; kuma Oshiomole zai iya zama musu cikas.

Zulum yace yayin martani ga El-Rufa'i: "Wani gwamnan APC ne ya yanke wannan shawara tare da kai? A ina da yaushe muka zauna muka amince da cewa shugaban jam'iyya yayi Murabus."

"Wannan fa abun kan 2023 ne. Suna son su nada wanda zasu iya juyawa matsayin shugaban jam'iyya. Shi yasa suka son tsige Oshiomole."

Sauran gwamnonin da suka goyi bayan Zulum sun hada da gwamnan Legas, Babajide Sanwoolu; gwamnan Osun, Gboyega Oyetola da gwamnan Ogun, Dapo Abiodun.

A wani labarin mai alaka, Tsohon dan takaran gwamnan Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya bayyana cewa wasu gwamnoni na kokarin tsige shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Adams Oshiomole domin daura tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari.

Yayinda yake magana da manema labarai a jihar Zamfara, Marafa yace gwamnonin na shirya hakan ne don kwace jam'iyyar domin siyasar 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel