Khadimul Islam: Ganduje ya sanya wa sabuwar gadar sama sunan wani babban malamin Islama

Khadimul Islam: Ganduje ya sanya wa sabuwar gadar sama sunan wani babban malamin Islama

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a ranar Asabar ya sanya wa sabuwar gadar sama ta Kofar Mata da ke tsakar birnin Kano, sunan wani babban malamin darikar Kadiriyya.

Gadar da a halin yanzu ake kan aikinta, ta ci sunan shugaban darikar Kadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara.

Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabin a taron shekara na darikar Kadiriyya da ake kira da "Maukibi".

Ya ce wannan karramawar ta biyo bayan gudummawar Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara a rainon musulunci da cigaban mutane.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamna Kalu ya yi magana daga gidan yari, ya fadi irin abincin da ake bashi

"Gwamnatin jihar ta yadda da jinjinawa mutane da suka taka rawar gani a jihar, matattu ko rayayyu. A don haka ne nake horarku da ku taya gwamnatin duba aikin gadar da ake yi tare da taimakawa gwamnati da addu'o'i," in ji Ganduje.

Hakazalika, wata takarda da daraktan yada labarai da huld da jama'a na gidan gwamnatin jihar Kano, Ameen K. Yassa a ranar Asabar, ya ce gadar na da tsawon 170.55 kuma na fara aikinta ne makonni kadan da suka gabata. Ana sa ran za a kammala gadar nan da watanni shida. A halin yanzu an ci kashi 35 na aikin.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, wannan ne kashi na 69 na taron darikar Kadiriyya ko kuma Maukibi a jihar Kano. An samu mutane daga kasashe daban-daban na Afirka da suka halarci taron.

A jawabin Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin ya roki Sheikh Nasiru Kabara da ya habaka kwalejin ilimi da ake ginawa zuwa matsayin jami'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel