Asirin wani dan yankan kai da ke haukar karya ta tonu (Hoto)

Asirin wani dan yankan kai da ke haukar karya ta tonu (Hoto)

- Asirin wani dan 'yan kai da ke karyar hauka ya tonu a karamar hukumar Ugheli na jihar Delta

- Asirinsa ya tonu ne bayan 'yan banga sun hange shi yana amsa waya yana magana tamkar mai hankali

- Daga bisani sunyi bi sahunsa har ya koma kasar gada da ya ke zaune kuma suka same shi da kokon kan dan adam da wayoyi da wasu kaya

An kama wani mutumi da ake zargin dan yankan kai ne da ke basaja a matsayin mahaukaci a karkashin gadar Otokutu da ke karamar hukumar Ugheli da Kudu na jihar Delta a ranar 12 ga watan Disamba.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana an kama shi da kokon kan dan adam tare da wayoyin tarho da wasu kayayyakin.

Asirin wani dan yankan kai da ke haukar karya ta tonu (Hotuna)

Wani mahaukacin karya da ke zargi da yankan kai
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Tirkashi: Matashi mai shekaru 19 dirka wa mahaifiyarsa cikin shege

Yan banga na unguwar ne suka bi sahun wanda ake zargin zuwa wurin da ya ke buya a karkashin gadar bayan sun hangi shi yana amsa waya tamkar mutumin da ke da cikakken lafiyar kwakwalwa.

Sai dai 'mahaukacin' ya jefar da daya daga cikin wayoyinsa na tarho cikin rafi yayin da ya lura tawagar jami'an tsaron sun gano dabararsa.

'Yan bangan sun far masa inda suka lakada masa dukkan tsiya kafin daga bisani suka mika shi hannun jami'an 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel