An kone wani saurayi kurmus, bayan ya daddatsa mutane 9 da adda, inda 7 daga cikin 'yan uwanshi ne na jini

An kone wani saurayi kurmus, bayan ya daddatsa mutane 9 da adda, inda 7 daga cikin 'yan uwanshi ne na jini

- Wani mutum mai suna Chigozie ya hadu da ajalinsa bayan da matasan yankinsu suka banka mishi wuta

- An gano cewa, matashin dan kasuwan ya haukace ne inda ya daddatsa mutane tara da adda

- Fusatattun mazauna yankin ne suka banka mishi wuta inda ya kone kurmus a matsayin maida martani

Wani mutum da ake zargin mahaukaci ne ya tarar da ajalinsa. Mutanen yankin ne suka banka mishi wuta inda ya kone kurmus.

Mazauna yankin sun aikata hakan ne bayan da ya hallaka mutane tara a yankin. Mutane bakwai daga ciki kuwa ‘yan gida daya ne.

An kone wani saurayi kurmus, bayan ya daddatsa mutane 9 da adda, inda 7 daga cikin 'yan uwanshi ne na jini
An kone wani saurayi kurmus, bayan ya daddatsa mutane 9 da adda, inda 7 daga cikin 'yan uwanshi ne na jini
Asali: Facebook

Mutumin da aka gano sunanshi da Chigozie Orusa ya azabtu kafin ya mutu, sakamakon wutar da aka banka mishi bayan da ya halaka mutane tara a Nempi, karamar hukumar Oru ta yamma ta jihar Imo.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Chigozie dan kasuwa ne a Onitsha kuma ya samu tabin hankali ne ba da dadewa ba. Abokanshi na Onitsa ne suka kamashi inda suka kaishi danginshi a Nempi. Yana samun kula tare da magungunan ciwon da ya addabeshi.

KU KARANTA: Tashin hankali: Bakanike ya dirkawa uwa da 'ya'yanta mata guda biyu cikin shege

Amma kuma, koda Chigozie ke shan magani, abun yana cigaba ne. A sa’o’in farko na ranar 8 ga watan Disamba, Chigozie ya sassara mutane 9 da adda. Bakwai daga cikin mutane taran kuwa ‘yan gida daya ne. Sun hada da kaka, matar kakan ta uku da kuma ‘yan uwa guda biyar. Sauran mutanen biyu kuwa makwabta ne.

A yayin mayar da martani ga kashe-kashen ne matasan yankin suka bankawa Chigozie wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel