Tashin hankali: Bakanike ya dirkawa uwa da 'ya'yanta mata guda biyu cikin shege

Tashin hankali: Bakanike ya dirkawa uwa da 'ya'yanta mata guda biyu cikin shege

- Mummunan lamarin ya faru ne a tashar yankin Iju da ke karamar hukumar Ifako-Ijaiye da ke jihar Legas

- Wani mutum mai suna Adesina ya dinga kwanciya da yaya, kanwa da mahaifiya don ‘gyaran kaddararsu’

- Babbar yayar ce ta garzaya gaban hukuma don sanar dasu. Hakan ya faru ne bayan da ta gano tana dauke da juna biyu

Mummunan lamarin ya faru ne a tashar yankin Iju da ke karamar hukumar Ifako-Ijaiye da ke jihar Legas. Da yawa daga cikin mazauna yankin sun jajanta aukuwar lamarin.

Matasan yankin ne suka cafke Adesina bayan da ya bayyana cewa ya san wata matashiyar yarinya a mace. Ya ce da taimakon mahaifiyarta ne wacce yake kokarin taimako.

Tashin hankali: Bakanike ya dirkawa uwa da 'ya'yanta mata guda biyu cikin shege

Tashin hankali: Bakanike ya dirkawa uwa da 'ya'yanta mata guda biyu cikin shege
Source: Facebook

A yayin zantawa da matashiyar budurwar mai shekaru 13 da yayarta mai shekaru 19, jaridar Puls ta gano cewa, Adesina ya yaudaresu dacewa matukar basu kwanta dashi ba, dan uwansu da ke kwance rai a hannun Allah bashi da lafiya, ba zai taba samun lafiya ba. Hakazalika, daya daga cikinsu zata haukace.

Daya daga cikin wacce abun ya faru da ita mai suna Opeyemi mai shekaru 19 ce ta samu kwarin guiwar kaiwa ‘yan sanda rahoto. Ta sanar da manema labarai yadda Adesina ke lalata da ita, kanwarta da mahaifiyarsu a daki daya. A wani lokacin kuwa a gaban idon mahaifiyarsu.

Tashin hankali: Bakanike ya dirkawa uwa da 'ya'yanta mata guda biyu cikin shege

Tashin hankali: Bakanike ya dirkawa uwa da 'ya'yanta mata guda biyu cikin shege
Source: Facebook

Kamar yadda ta bayyana, ta ce: “Ina zama ne a Ibadan tare da dan uwan mahaifina inda nake koyarwa kuma ina koyon dinki. A makonni uku da suka gabata, mahaifiyata ta zo da Adesina. An bukaci in je bikin ‘yar yayata, A don haka ne na kwashi kayana muka tafi.”

KU KARANTA: Ta debo da zafi: Bazan iya aurar mutumin da bashi da akalla motoci 3, gidaje 2 da kuma tsayyen kasuwanci ba - Budurwa

“Abinda ban sani ba shine, duk karya ne. A lokacin da na isa Legas sai labari ya sauya. Adesina ya ce, ya hango cewa kakata mayya ce kuma yana kokarin gyara kaddararmu. Ya ce in har inaso in kubuta, dole ne in yarda ya kwanta da ni. A halin yanzu ban ga al’adata ba don sati biyu kenan da ya fara kwanciya dani.”

Ta kara da cewa, “A lokacin da nake koke, kanwata ta sanar dani cewa ita ma yana kwanciya da ita.”

A bangaren kanwar, ta bayyana cewa ta amince Adesina ya dinga kwanciya da ita ne bayan da dan uwanta mai suna Peter ya fadi ciwo. Ya sanar da ita cewa ana bukatar jinin budurci don tseratar da rayuwarshi.

A bangaren mahaifiyar, ta bayyana cewa, ta fara kwanciya da Adesina ne don samun lafiyar mijinta a lokacin da ya fadi rashin lafiya. Hakan kuwa bai sa mijin nata ya samu lafiya ba don daga bisani mutuwa yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel