Yadda babban abokin ango ya kashe aure sa'o'i kadan bayan daura auren

Yadda babban abokin ango ya kashe aure sa'o'i kadan bayan daura auren

Wata amarya mai shekaru 26, Erin Mason-George ta nemi a raba aurenta da mijinta awanni kadan bayan kammala liyafan cin abinci na auren bayan duka da cin mutunci da ita da 'yan uwanta suka sha.

Tun watanni hudu da suka gabata ne dan uwan mijin Erin kuma babban abokinsa Tomos Rydian Wilson ya ci mutuncin ta kafin daga bisani ya yi wa 'yan uwanta biyu da mahaifiyarta duka bayan ya yi tatil da giya.

An ruwaito cewa an jiyo Tomos yana cewa tun farko bai kamata dan uwansa ya auri Erin ba yayin da ya ke rike da rigar aurenta sannan ya janyo ta daga saman bene zuwa kasa.

Abokan angon, Steffan Wilson da amaryar, Erin sun shaida wa Mail Online cewa maauratan sun yanke shawarar raba auren ne bayan dukan da babban abokin angon ya yi wa iyalan amarya.

DUBA WANNAN: Me yayi zafi? Amarya ta fada rijiya ana gobe bikinta a jihar Kano

Babban abinda ya saka amaryar ta nemi a raba auren shi ne yadda angonta ya bi babban abokinsa suka tafi gida tare a daren da ya yi mata duka a maimakon ya lalashe ta ko ya nuna damuwarsa kan afkuwar lamarin.

Wani abokin maauratan da ya nemi a sakayya sunansa ya ce, "Auren ya mutu a kwana daya hakan abin mamaki ne. Ba za su iya neman kotu ta raba auren ba ma domin ba su dade da aure ba. Na ji an ce za su soke auren ne kawai."

"Mijin yana da zabi, ko ya zabi amaryarsa ko kuma mahaifinsa da dan uwansa. Auren ya mutu bayan ya zabi yan uwansa."

An gurfanar da Tomos a gaban wata kotu da ke Aberystwyth a farkon wannan makon, kuma an same shi da laifuka biyar na duka da kuma lalata kayayaki. An yanke masa hukuncin watanni 12 yana yi wa unguwansu hidima kuma an umurci ya biya Erin da yar uwanta diyar fam 250 kowannensu kuma ya biya mahaifiyarsu da dayan yar uwanta fam 100 kowannensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel