Alkalin Alkalan Najeriya ya nemi a sanya dokokin Musulunci a tsarin mulkin Najeriya

Alkalin Alkalan Najeriya ya nemi a sanya dokokin Musulunci a tsarin mulkin Najeriya

Babban Alkalin Alkalan Najeriya, mai sharia Ibrahim Tanko Muhammad ya nemi a gudanar da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda zai kunshi tanade tanaden shari’ar Musulunci a cikinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Alkali Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da yake bude taron Alkalan Najeriya karo na 20 dake gudana a tsangayar ilimin sharia na jami’ar Ahmadu Bello, inda ya yi jawabi a kan ‘Adana bayanan kwangila a mahangar shariar Musulunci: Yadda ake yi, ya aka yi shi a baya’.

KU KARANTA: Yan Najeriya 4 sun shiga hannu a kasar Amuka kan satar naira biliyan 6.5

Cibiyar ilimin shariar Musulunci ta jami’ar ABU tare da hadin gwiwar cibiyar sharia ta kasa ne suka shirya taron, inda Alkalin Alkalai ya yi kira ga malamai dake koyar da ilimin sharia su dauki gabaran ganin an sauya yadda ake koyar da ilimin shariar Musulunci.

Da yake jawabi a yayin taron, Alkalin Alkalai Ibrahim Tanko Muhammad, wanda ya samu wakilcin babban alkalin shariar Musulunci na jahar Neja, Muhamamd Danjuma, ya bayyana cewa hakan zai yiwu ne kadai idan jami’o’i za su baiwa shari’ar Musulunci tsangayarsa ta daban.

“Kamar yadda muka sani ne, akwai wasu sassa na kundin tsarin mulki da suka bayar da daman dabbaka shari’ar Musulunci a kan kai, amma banda wannan babu wani tanadi, amma kuma muna da yawan da zamu iya neman a gudanar da wannan sauyi don ya dace da bukatar Musulmai.

“Ko ba komai idan aka samu karin Alkalai da suka karanci shari’ar Musulunci, hakan zai basu daman fahimtar shari’un dake gabansu da suka danganci hukunce hukuncen shariar Musulunci.” Inji shi.

Haka zalika Alkalin ya yi kira da koma koyar da ilimin shariar Musulunci da harshen larabci ba da harshen turanci ba duba da muhimmancinsa, wannan kuma kalubale ne ga malamai, a cewarsa.

A nasa jawabin, shugaban jami’ar ABU, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana cewa ire iren wannan taro na masu ilimi wani dama ne na kara ma juna sani, tare da fadada ilimin mahalarta ta yadda zai amfani kowa da kowa, shi yasa jami’ar ta bayar da goyon bayanta ga taron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng