Tirkashi: Karuwa ta shiga kotu da katon maciji a lokacin da ake shirin yanke mata hukunci

Tirkashi: Karuwa ta shiga kotu da katon maciji a lokacin da ake shirin yanke mata hukunci

- A yankin Mutare na kasar Zimbabwe ne aka cafke wata karuwa da laifin ajiye zabgegiyar mesa a dakinta

- An zargi karuwar da amfani da mesar mai tsawon mita 6 da yin sihiri tare da surkulle

- Tuni hukumar adana dabbobi ta kasar ta gurfanar da ita a kan laifin ajiye mesar a cikin gidanta

Wata karuwa ta gurfana a gaban kotun majistare ta Mutare bayan da ake tuhumarta da laifin ajiye dabba mai hatsari a muhallinta.

An gano cewa, tana amfani da Mesar ne mai tsawon mita 6 don yin sihiri ga masu nemanta.

Ta adana macijin ne a mazauninta da ke Green Gate Lodge, inda take harkar karuwancinta.

Bayan tuhumarta da kotu ta yi, ta bayyana cewa ba macijinta bane, na Loice Samhere ne wacce itama aka cafkota.

Mutane sun yi cincirondo a kotun bayan da aka iso da Mesar har kotu don ta zama shaida. Wannan lamarin dai ya faru ne a Zimbabwe. Ma'aikatan kula da wajen ajiye dabbobi ne suka yi wa Mesar rijista don adanata, saboda alkalin yace bashi da wajen adanata.

KU KARANTA: Jerin matan arewa guda 5 da suka yi fice wajen kare hakkin Dan Adam a duniya

An mayar da dabbar mai hatsari zuwa gidan tarihi na Mutare don adana.

Karuwar mai suna Queen Mpofu an garkameta ne har zuwa ranar 20 da watan Disamba don cigaba da shari'ar.

Duk da an bukaci belin Mpofu tare da Samhere, alkalin ya yi watsi da wannan bukatar.

Ana zarginsu ne da karantsaye ga dokokin ma'adanar dabbobi masu hadarin gaske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel