Rikici a fadar shugaban kasa: Ba zan sake lamuntan rainin wayonka ba - Aisha Buhari tayi fito na fito da Garba Shehu

Rikici a fadar shugaban kasa: Ba zan sake lamuntan rainin wayonka ba - Aisha Buhari tayi fito na fito da Garba Shehu

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, ta saki bama-baman kalamai kan mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Ta bayyana yadda yake yiwa maganganun karya da ake yiwa Buhari rikon sakainar kashi maimakon bayyanawa al'umma da wuri cewa ba gaskiya bane.

Hakazalika Aisha ta laburta cewa lokacin da aka shirya kaidin bidiyon da diyar Mamman Daura ta yada a yanar gizo inda ake kokarin fahimtar da yan Najeriya cewa an hanata shiga fadar shugaban kasa lokacin da ta dawo Najeriya bayan dogon hutun da ta dauka, Garba Shehu yayi shiru duk da cewa ya san gaskiyar lamarin maimakon karyata labarin.

Bugu da kari lokacin da ake rade-radin cewa Buhari zai kara aure, Aisha ta ce Garba Shehu ya sake shiru amma yayi gaggawan sakin jawabi lokacin da ya samu labarin cewa za ta dawo gida.

A karshe, ta gargadi mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu, cewa ya sani daga yanzu ba zata sake lamuntan raini wayonsa ba.

DUBA NAN Yanzu-yanzu: Garba Shehu ya daina biyayya ga Buhari - Aisha Buhari

Tace: "Tirke-tirken baya-bayan ne da yayi na fito na fito da iyalan shugaban kasa ta hanyar daukan nauyin wasu yan jarida masu bata sunana da na 'yayana."

"Bisa ga mayar da biyayyansa kan wasu yan tsirarun mutane, ya bayyana cewa babu yarda da amince tsakaninsa da iyalaina saboda cin mutuncin da a janyowa fadar shugaban kasa da iyakan shugaban kasa...."

"Garba Shehu, ya sani daga yanzu ba zata sake lamuntan wadannan halayensa ba."

"A yau, ko babu kasafin kudi, zan iya gudanar da ayyukan jin kai da nikeyi. Da kasashen da suka cigaba ne, kamata yayi Garba Shehu yayi murabus saboda ya wuce gona da iri."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel