Tabdijam! Hisbah ta saki yan daudu guda 30 bayan sun yi sallar dare raka’a 40

Tabdijam! Hisbah ta saki yan daudu guda 30 bayan sun yi sallar dare raka’a 40

Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta kama wasu gungun yan daudu guda 30 a yayin da suke shirin aiwatar da wata mummunan badala a wani gida dake cikin birnin Kano, kamar yadda rahoton BBC Hausa ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Dakta Aliyu Musa Kibiya ne ya tabbatar da haka ga majiyar Legit.ng inda yace da fari jami’an Hisbah sun fara kama wani matashin dan daudu ne, inda a wayarsa suka jiyo wani shiri da abokansa yan daudu suke yi na yin gangami a wani gida.

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya sallami Malamai 200 da basa zuwa aiki a jahar Borno

“Bayan sun gama taruwa don yin wannan biki ne sai hukumar Hisbah ta dira gidan, inda ta yi nasarar kamasu duka, kuma wasu daga cikinsu sun tabbatar mana da cewa dukkaninsu yan daudu ne banda mutane uku, kuma abin haushi iyayensu ma basu san suna daudu ba.” Inji shi.

Shugaba Kibiya ya kara da cewa: “Alhamdulillahi mun zaunar dasu sun yi ta yin sallolin nafila da ma tsayuwar dare ba don komai ba sai domin wani lokaci idan kaga dan adam na aikata wani mummunan aikin, zuciya ce ta lalace.”

Daga karshe shugaban yace kowanne daga cikin yan daudun sai da ya yi salla raka’a arba’in arba’in, inda yace dama hakan na daga cikin tanadin da hukumar Hisbah ke yi ma masu laifi, saboda sallah na korar duk wani shaidani dake tattare da mutum.

A wani labarin kuma, uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, ta yi rabon kayan abinci da kudi ga marayu da gajiyayyu a jahar Adamawa, wanda suka tasan ma miliyoyin nairori.

Aisha Buhari wanda ta samu wakilcin Hajiya Fatima Rafindadi ta yi rabon kayan ne a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba a garin Yola, inda ta shaida cewa sun yi rabon ne daga cikin ayyukan gidauniyar Aisha Buhari ta ‘Future Assured’.

Aisha tace babbar manufar rabon kayayyakin shi ne bayar da gudunmuwa ga ayyukan gwamnatin tarayya na inganta rayuwar yan Najeriya, musamman wadanda suka fito daga yankunan karkara. Kayan sun hada da buhunan shinkafa, doya, man girki da atampopi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel