Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban AMCON, da Buhari ya nada yau

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban AMCON, da Buhari ya nada yau

A yau Talata, shugaba Muhammadu Buhar ya nada Mista Edward Adamu a matsayin sabon shugaban hukumar raya dukiyoyi a Najeriya AMCON.

Adamu zai maye gurbin Dakta Muiz Banire, da aka nada a watan Yulin 2018.

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban AMCON, da Buhari ya nada yau
Edward adamu
Asali: UGC

Ga abubuwa 8 da ya kamata ku sani akansa:

1. Edward Lametek Adamu kwararran masanin lissafin gine-gine ne kuma dan kasuwa

2. An haifeshi ranar 22 ga Yunin 1959 a Kaltungo jihar Gombe

3. Ya samu digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya

4.Ya tafi karin ilimi a jami'o'i daban-daban a Amurka, Faransa, da Swizalan

5. Yana daya daga cikin mambobin kungiyar kwararrun masu kiyasin gine-gine a Najeriya

6. Adamu ya fara aiki da babbar bankin Najeriya CBN tun shekarar 1992

7. A awatan Febrairun 2018, an nadashi matsayin mataimakin gwamnan babbar bankin Najeiry CBN

8. Edward Adamu nada aure da yara hudu

A wani labarin daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Muhammad M. Nami a matsayin shugaban hukumar kudin shiga ta tarayya, FIRS.

Nami zai maye gurbin Tunde Fowler, wanda wa'adin mulkinsa ya kare a ranar Litinin da ta gabata.

Sabon shugaban hukumar, kwararre ne a bangaren haraji kuma ya kammala karatunsa ne a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel