Auren buta: Dan shekara 75 ya auri yar shekara 82 a jihar Kano

Auren buta: Dan shekara 75 ya auri yar shekara 82 a jihar Kano

Wani dattijo dan shekara 75 mai suna Muhammad Liti ya raya sunnah da masoyiyarsa yar shekara 82, Fatima Malam bayan sun kwahse watanni takwas suna watsa soyayya a jihar Kano.

A cewar wani rahoto da gidan rediyon Dala FM ta koro ranar Litinin a Kano, an yi daurin auren ne a daren Lahadi, 9 ga watan Disamba a Kan Fako, garin Dorayi dake karamar hukumar Gwale.

Rahoton ya kara da cewa an daurawa Muhammad Liti aure da sabuwar amaryarsa mai soya kosai da wainar Rogo kan sadaki N10,000.

Bugu da kari, jama'a, yan uwa da abokan arziki sun yi cincirindo a wajen waliman domin shaida wannan biki mai albarka.

Hakazalika sun cashe tamkar matasa inda amaryar taci kwalliya irin ta amare.

Angon, Muhammad Liti ya bayyana farin cikinsa kan samun abokiyar zama kuma yace ya aureta ne bisa ga soyayyar da yake mata na gaskiya.

A nata bangaren kuwa, Amarya Fatima Malam ya yi alkawarin yin biyayya ga mijinta duk da cewa ya girmeshi da shekaru takwas.

Tace: "Farin ciki na a yau tamkar na maniyyacin da zai tafi Makkah, Ina matukar farin ciki saboda na samu masoyi. Ina alkawarin cewa zan yi masa biyayya."

"Zamu zauna matsayin miji da mata kuma zamuyi dukkan abinda ma'aurata keyi, ba kawai kai masa buta bayi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel