Osinbajo ya tafi kasar Dubai domin ganawa da yariman kasar mai jiran gado

Osinbajo ya tafi kasar Dubai domin ganawa da yariman kasar mai jiran gado

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya shilla birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa, UAE, wanda aka fi sani da Dubai, domin gabatar da jawabi a kan muhimmancin addini wajen hada kan jama’a.

Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 8 ga watan Disamba, inda yace Osinbajo zai gabatar da jawabi a yayin taron ne a matsayin babban mai gabatar da jawabi.

KU KARANTA: Jerin ‘Ya ‘yan Shugaba Buhari da Makarantun da su ka yi karatu

Haka zalika Osinbajo zai samu damar ganawa da jagoran gwamnatin kasar, kuma yarima mai jiran gado, Sheikh Mohammed Bin Zayed Al Nahyan, inda zasu tattauna a kan batutuwan da suka bukatun kasashen biyu ta fannin diflomasiyya da kuma tattalin arziki.

Gwamnatin kasar Dubai ce ta shirya wannan taro kamar yadda ta saba shekara shekara, manufar taron shi ne samar da hanyoyin inganta zaman lafiya a tsakanin al’ummomi musulmai a duk fadin duniya.

Gwamnatin Dubai tace: “Taron na 6 zai fara ne da daura tattaunawa daga inda taron bara ya tsaya, shawarwarin da aka zartar da kuma bayyana godiya ga gwamnatin Dubai bisa tabbatar da shekarar 2019 a matsayin shekarar hakuri da juna.

“Manufar taron na 6 shi ne bayar da dama ga shuwagabannin duniya su samar da wani sabon tsari game da hakuri da juna, wanda ke dauke da adalci da tausaya ma juna, tare da nuna muhimmancin haka a addinance.”

Daga karshe sanarwar ta karkare da bayyana cewa mataimakin shugaba Osinbajo zai dawo gida Najeriya a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel