Mata 800,000 ke fama da ciwon yoyon fitsari a Najeriya - Majalisar dinkin duniya

Mata 800,000 ke fama da ciwon yoyon fitsari a Najeriya - Majalisar dinkin duniya

Kwamitin majalisar dinkin UNFPA ta ce akalla mata 800,000 na fama da ciwon yoyon fitsari a fadin Najeriya.

UNFPA ta kara da cewa kowani shekara ana samu karuwan mutane 20,000 da suka kamu da ciwon kuma akwai bukatar maganceshi da kawo karshenshi a Najeriya.

UNFPA tare da hadin kan ma'aikatar kiwon lafiyan jihar Kaduna na shirin shirya taron awaya da kai na kwana daya a jihar.

Shugabar ofishin UNFPA na yankin Arewacin Najeriya, Mariama Barboe, ta saki jawabi inda ta bayyana cewa za'a fara taron ranar 18 ga watan Disamba, 2019 da atisayen jijjiga jini a cikin garin Kaduna.

Tace: "Wannan kiyasi abin damuwa ne kuma ba zamu lamunci hakan ba saboda mata 400,000 zuwa 800,000 na zama da ciwon yoyon fitsari a Najeriya."

Bugu da kari, ana samun karuwan mutane 12,000 zuwa 20,000 a kowani shekara."

A wani labarin mai alaka da hakan, Shugaban asibitin magance ciwon yoyon fitsari ta kasa dake jihar Bauchi, Umar Ibrahim, ya bayyana cewa yankin Arewa maso gabashin Najeriya ta fi sauran yankunan kasar yawan mata masu fama da ciwon.

Ya bayyana hakan a hirar da yayi da manema labarai ranar Talata a garin Ningi inda yace an kafa asibitin ne don jinyan al'ummar jihohi shida amma mutane na zuwa daga dukkan sassan Najeriya.

Ciwon yoyon fitsari wanda akafi sani da VVF ciwon ne da ya shafi mata a lokacin haihuwa inda fitsari zai rika zuba ba tare sun sani ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel