Daga karshe, Saudiyya ta biya kudin diyyan Mahajjatan Nijeriyan da suka mutu a Harami a 2015

Daga karshe, Saudiyya ta biya kudin diyyan Mahajjatan Nijeriyan da suka mutu a Harami a 2015

Bayan shekaru hudu da mumunan hadarin da yayi sanadarin shahadar akalla yan Najeriya shida a filin harami yayinda suke gudanar da aikin hajji, gwamnatin masarautar Saudiyya ta cika alkawarinta.

Za ku tuna cewa a ranar 11 ga watan Satumban 2015, karafuna gini sun rikito kan mahajjata a cikin haramin Makkah inda akayi asarar rayuka kuma da dama sun jikkata.

Najeriya ta yi rashin mahajjata shida daga jihar Gombe, Kaduna da Katsina.

Hukumar jin dadin alhazan Najeriya, NAHCON, ta bayyana cewa jakadan Najeriya zuwa Saudiyya Muhammad Isa Dodo, ya bayyana hakan a Jeddah, inda akayi zaman yarjejeniya kan shirye-shiryen Hajjin 2020.

Hukumar ta tabbatar da cewa an biya kudin mutane biyar da suka rasu da biyu da suka samu raunuka kuma za'a mika kudaden ga iyalan mamatan.

Karamin ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Zubairu Dada, ya mika godiyar gwamnatin Najeriya, ga ministan Hajji da Umrah na kasar Saudiyya, Muhammad Bn Saleh Benten.

KU KARANTA: Yadda aka tsinci malamin jami'a a mace cikin ofishinsa

A bangare guda, Hukumar kula da aiyukan Hajji taa Najeriya, NAHCON, a ranar Asabar tace ta samu kujeru 95,000 na maniyyatan aikin Hajji na shekarar 2020.

Wannan na kunshe ne a takardar da shugabar bangaren hulda da jama’a ta hukumar NAHCON, Fatima Usara, ta ba manema labarai a garin Abuja.

Ta ce, an sa hannu a yarjejeniya tsakanin karamin ministan harkokin waje na Najeriya, Zubairu Dada da kuma ministan aiyukan Hajji da Umara, Saleh Benten.

Ta ce, an sa hannu a kan yarjejeniyar ne a ranar 5 ga watan Disamba, a shirye-shiryen aikin Hajji na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel