Yadda aka tsinci malamin jami'a a mace cikin ofishinsa

Yadda aka tsinci malamin jami'a a mace cikin ofishinsa

An tsinci gawan wani malamin tsangayar ilmin motsa jiki da kiwon lafiya a jami'ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, jihar Osun mai suna, Mista Nicholas Igbokwe, da safiyar Asabar, 7 ga watan Disamba, 2019.

An tsince gawar Mista Nicholas, ne cikin ofishinsa da safe ba tare da wani rauni ko alamun ciwo ba.

Rahotanni sun bayyana cewa Mista Nicholas ya isa ofis cikin koshin lafiya da safiyar jiya kafin mutuwarsa.

Jami'in hulda da jama'a na jami'ar, Abiodun Olarenwaju, ya tabbatar da labarin inda ya kara da cewa an garzaya da gawar dakin ajiye gawawwaki.

Yace: "Dan ban tausayi mun rasa shi. Babu wanda yayi tunanin haka. An kawoshi asibiti da safen nan a mace."

Daya daga cikin abokan aikinsa ya siffanta Nicholas matsayin mutum mai saukin kai kuma mutuwarsa babban rashi ne ga jami'ar.

KU KARANTA: Yadda AbdulAziz Yari ya biya kansa N350m ana saura kwana biyu ya sauka mulki

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya taya shagon duniya, Anthony Joshua, murnan nasara a damben da ya gudana a daren Asabar tare da dan kasar Mexico, Andy Ruiz.

Shugaba Buhari ya jinjinawa Anthony Joshua kan kawo farin ciki ga miliyoyin yan Najeriya dake gida da kasashen waje da sukayi tsayin daka wajen ganin cewa za kwato bel-bel din da ya rasa watanni shida da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel