Yadda AbdulAziz Yari ya biya kansa N350m ana saura kwana biyu ya sauka mulki

Yadda AbdulAziz Yari ya biya kansa N350m ana saura kwana biyu ya sauka mulki

A makonnin baya, tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Abubakar Yari, ya rubuta wasika ga gwamnan jihar, Muhammad Matawallen Muradun, kan rike masa kudin alawus dinsa na milyan goma kowani wata.

Hakan ya sa yan majalisar dokokin jihar soke dokar kai tsaye kuma gwamnan ya rattafa hannu ba tare da bata lokaci ba.

Yayinda yake rattaba rattaba hannu, gwamna Matawalle ya tuhumci Yari da biyan kansa N360m daga kudin fanshon jihar.

Takardun shaida daga bankin Zenith ya bayyana cewa AbdulAziz Yari ya biya kansa N350m kafin ya sauka daga mulki.

An kwashe kudaden ne a ranar 27 ga Mayu, 2019.

Hakazalika, an biya mataimakin gwamnan, Ibrahim Wakalla, milyan 175 a ranan.

Takardun sun nuna cewa an yi amfani da kudin wajen sayawa Yari wani gida a unguwar Maitama dake Abuja, kuma hakan yayi daidai da dokar fanshon jihar.

Matawalle yace: "Babu wani dalilin da zai sa jiha ta rika biyan tsaffin shugabanninta wadannan makudan kudi N702 million a shekara alhalin yan fansho na mutuwa a jihar."

A watan Nuwamba, Tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, ya bayyana cewa magajinsa, gwamna Bello Matawalle, ya hanashi kudin fansho da alawus dinsa a matsayin tsohon gwamna kamar yadda dokar jihar ta tanada.

A wasikar da ya aikawa gwamnan, Abdulaziz Yari, ya bukaci gwamna Matawalle ya biyashi kudaden saboda babu wani dalilin da zai sa ya rike masa kudi.

Yari ya ce tun da ya sauka daga mulki, sau biyu kacal aka biyashi kudin kula da kansa na N10m a wata.

Ya ce dokar jihar ta tanadi baiwa tsaffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni, tsaffin kakakin majalisa, da mataimakansu, alawus a ko wani wata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel