Yadda magidanci ya sumar da matarsa da duka bayan ya kama ta da kwarto a gidansa

Yadda magidanci ya sumar da matarsa da duka bayan ya kama ta da kwarto a gidansa

- Jami'an 'yan sanda sun cafke wani mutum mai suna Kofi Bandoli dan kasar Ghana

- Ana zarginsa ne da sumar da saka matarsa doguwar suma saboda mugun dukan da ta sha a hannunsa

- Ya kamata matarsa ne dumu-dumu da masoyinta suna lalata a kan gadon aurensu

Jami'an 'yan sanda sun cafke wani mutumi a kan laifin yi wa matarsa mugun duka har ta suma bayan da ya kamata dumu-dumu tana lalata da kwarto a kan gadonsu na aure.

Mutumin mai suna Kofi Bandoli mai shekaru 35 dan asalin kasar Ghana, ya shiga hannuna jami'an tsaro. 'Yan sandan yankin Awutu Bereku ne suka cafke wanda ake zargin.

An gano cewa, mutumin ya je aiki ne kuma sai ya yi kokarin kira matarsa don sanar da ita wani bayani amma sai bai sameta ba. Hakan ce ta sa dole ya garzaya gida don ganin ko meye ya faru da ita saboda ba halinta bane.

DUBA WANNAN: Waiwaye: Manyan jarumai 5 mata na Kannywood da su kayi tashe a baya

A yayin da ya kusanci daki, sai yaji wani gurnani. Shigarsa dakin ke da wuya ya tsinci matarsa da masoyinta suna sha'aninsu a kan gado.

Fushi da tsananin harzuka da ya yi ne suka da Bandoli ya kama matarsa da duka. Ya yi mata mugun dukan da ya yi sanadin da ta fada doguwar suma. Tuni masoyin nata ya hanzarta barin inda lamarin ya faru.

A halin yanzu, matar na kwance rai a hannun Allah a asibitin Awutu Breku. Shi kuwa Bandoli yana garkame hannun jami'an tsaro inda zasu mika shi gaban kuliya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel