Yadda dalibai suka dirka wa malaminsu abin barasa don suyi satar jarrabawa

Yadda dalibai suka dirka wa malaminsu abin barasa don suyi satar jarrabawa

Wani dalibin karamar makarantar Sakandare da ke Alausa a jihar Legas ya firgita mutane da wani bayani da yayi. Yaron ya sanar da mutane yadda dalibi dan uwanshi ya ba malamai kwaya don samun satar jarabawa.

Wannan bayanan an samesu ne a taron da kungiyar mamallakan makarantun kudi ta jihar Legas ta shirya. An gudanar da taron ne a dakin taro na Adeyemi Bero da ke Alausa a ranar Litinin.

Taron an mishi take da, “Illolin ta’amalli da miyagun kwayoyi ga matasa.” A yayin taron, an samu tambayoyi da amsoshi inda yara masu kwarin guiwa suka tashi suka dinga tambayoyin.

Ya ce: “Ta yaya zamu shawo kan yadda dalibai ke shayar da malamai kwayoyin don samun satar jarabawa?”. Yaron ya bayyana cewa, matukar suka saka kwaya cikin abun shan malami, sai bacci ya yi awon gaba dashi sannan su samu su yi satar jarabawa. Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta duba lamarin.

DUBA WANNAN: Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

Bayan yaron ya gama bayanin, wata mahaifiya ta karba amsa kuwwar inda ta yi bayanin yadda dan makwabtanta ke ta’ammali da miyagun kwayoyi kuma abun na damunta.

A yayin mayar da martani, babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi na jihar Legas, Mrs Abosede Adelaja ta ce, kamata ya yi iyaye da malamai su sa ido a kan yaransu. Ta kara da cewa, tabarbarewar tarbiya karuwa take yi a cikin al’umma.

Ta ce: “Ba zan musanta ba, saboda idan yaran ba su gani ba ko sun ji ba, ba zasu sanar ba. Akwai bukatar dukkanmu mu koma don kula da yaranmu. Wannan alhakin ya rataya ne a kan iyaye, masu kula da kuma malamai. Idan har muka ga wani mummunan hali a wajensu, kamata ya yi mu gaggauta daukar mataki. Sau da yawa iyaye na neman kudi ne suna mantawa da tarbiya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel