Zan bi diddigin kisan matashi Mus'ab har sai gaskiya ta yi halinta - Sheikh Isah Ali Pantami

Zan bi diddigin kisan matashi Mus'ab har sai gaskiya ta yi halinta - Sheikh Isah Ali Pantami

- Ministan sadarwar Najeriya, Dakta Ali Pantami, ya sha alwashin bincike a kan kisan da wani dan sanda a Kano ya yi wa wani saurayi

- A ranar Talata ne wani dan sanda a jihar Kano ya hallaka wani saurayi har lahira bayan 'yar takaddama da ta shiga tsakaninshi da dan sahu

- Ministan ya wallafa a shafinshi na tuwita, cewa da izinin Ubangiji sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi a kan lamarin kisan

Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa zai bi ba'asin yadda kisan Mus'ab Sammani ya kasance. Zai kuma bi hakkin kisan har sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi.

Mus'ab Sammani dai saurayi ne a birnin Kano wanda dan sanda ya harbe da bindiga sakamakon wata 'yar hayaniya da ta hada shi da dan sahu.

Sheikh Pantami ya wallafa a shafinshi na tuwita, ya sha alwashin bin ba'asin kisan saurayin don gano gaskiyar Lamarin.

A ranar Talata da ta gabata ne, wani dan bindiga dadin dan sandan da ke aiki da wani banki a Kano, ya kashe saurayi mai suna Mus'ab Sammani.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka labarta, Mus'ab sun tafka takaddama ne da wani dan sahu bayan da mai keken ya gogar mishi mota a Niger Avenue, ta Mallam Kato Square.

KU KARANTA: Aikin da Buhari yayi a Najeriya yafi na shekaru 16 da Obasanjo, 'Yar Adu'a da Jonathan suka yi akan mulki - Sagay

Dan sandan da ake zargi, ya ga mazajen na hayaniya mai zafi sai ya gangara don sasanci. Ya umarci Mus'ab da ya sauke motarshi daga kan titi. Lokacin da saurayin ya shiga zai tada motar, kawai sai dan sandan ya sakar mishi harsashi inda ya bulla ta gilashin motar ya samu Mus'ab a wuya. A take yace ga garinku.

An hanzarta mika shi asibitin Mallam Aminu Kano, amma sai aka bayyana tabbas mutuwa ya yi.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da aukuwa lamarin kuma ya ce an cafke dan sandan tare da fara gudanar da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel