Wa'iyazubillah: An kama dan sanda a lokacin da yake tsakiyar lalata da gawa

Wa'iyazubillah: An kama dan sanda a lokacin da yake tsakiyar lalata da gawa

- Wani jami’in dan sanda a birnin Los Angeles na cikin tsaka mai wuya, bayan da aka ganshi yana latsa nonon gawar wata mata

- An yi wa jami’in dan sandan kiran gaggawa ne inda suka isa gidan matar suka tarar ta mutu

- Tuni dai hukumar ‘yan sandan suka dakatar da jami’in aiki tare da gaggauta fara bincike a kan lamarin

Wani jami’in dan sanda a birnin Los Angeles na cikin tsaka mai wuya. An samu bidiyon dan sanda yayin da yake shafa jikin wata mata matacciya.

Kamar yadda rahoton da jaridar Los Angeles Times ta bayyana, lamarin ya faru ne a lokacin da dan sandan da abokin aikinshi suka amsa kiran gaggawa a kan cewa akwai yuwuwar wata mata ta rasu a wani yanki na birnin.

A lokacin da aka tabbatar da rasuwar matar, daya jami’in ‘yan sandan ya koma mota don dauko wani abu. Shi kuwa wanda ake zargin ya kashe na’urar bidiyon da ke jikinshi inda ya fara taba nonon matar, jami’an LAPD suka ce.

KU KARANTA: Bidiyo: Saurayi na tsakar lalata da karuwa aljanunta suka tashi sai ya koma addu'a

Na’urorin nadar bidiyo da sauti na jami’an LAPD din na nadar hoto da sauti ne mintuna biyu kafin a kunnasu. “Tuni muka sa a fara bincike a lokacin da muka gano faruwar lamarin, kuma mun bukaci jami’in dan sandan da ya dakata da aiki,“ kakakin ‘yan sanda Josh Rubenstein ya sanar da manema labarai.

Rubenstein ya kara da cewa, ba zai iya cigaba da tsokaci a kan lamarin ba saboda wasu aiyuka da ke jiranshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel