Gungun yan bindiga 2,000 sun mika makamansu ga gwamnan Zamfara

Gungun yan bindiga 2,000 sun mika makamansu ga gwamnan Zamfara

Akalla yan bindiga dadi guda 2,000 ne suka tuba, suka kuma mika wuya a yankin Gusau na jahar Zamfara, inda suka mika makamansu ga gwamnan jahar, Bello Muhammad Matawalle.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito akalla bindigu guda 190 yan bindigan suka mika ma gwamnan a garin Gusau, wanda hakan ke alanta sun tuba daga miyagun da suke tafkawa a baya.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kwashe miliyoyin kudi bayan sun kashe ‘Dan canji’ a Abuja Babban mashawarcin gwamnan a kan harkar watsa labaru, Zailani Bappa ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Alhamis, 5 ga watan Disamba a fadar gwamnatin jahar.

Badppa yace babban mashawarcin gwamnan a kan harkokin tsaro, Abubakar Dauran ne ya jagoranci tubabbun yan bindigan zuwa fadar gwamnatin domin su gana da gwamnan, inda ya tabbatar ma gwamnan da cewa sun tuba, kyakkyawar tuba.

Guda daga cikin shuwagabannin yan bindigan, Sani Shaidan yace sun samu kwarin gwiwar tuba ne duba da ayyukan da gwamnatin jahar take gudanarwa, inda yace gwamnatin data shude bata damu walwalarsu ba.

Shaidan ya kara da cewa sun gamu da take taken gwamnatin Matawalle cewa da gaske take don magance matsalolin da suka addabi jahar, don haka suka yanke shawarar bada gudunmuwarsu ga samar da zaman lafiya a jahar.

A nasa jawabin, Gwamna Matawalle ya tabbatar ma matasan cewa a shirye gwamnatinsa take ta yi duk mai yiwuwa don samar da dawwamammen zaman lafiya a jahar, sa’annan ya yi kira garesu dasu kafa kungiyoyi da zasu sanya idanu a kan duk miyagun da basu rungumi zaman lafiya ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel