Miyagu sun karbe kasa daga hannun mu - Aisha Buhari

Miyagu sun karbe kasa daga hannun mu - Aisha Buhari

Aisha Buhari, matar shugaba Muhammadu Buhari, ta ce 'miyagun mutane' sun karbe mulkin kasar daga hannun mutanen da ya dace su rika 'tafiyar da ragamar mulkin kasar' kamar yadda The Cables ta ruwaito.

Aisha ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin hirar wayar tarho da aka yi da ita a wani shiri na Television Continental (TVC).

Ta ce bai dace wadanda ya kamata su rika tafiyar da gwamnati suyi shiru ba yayin da wasu mutane ke amfani da kafafen sada zumunta suna kokarin bata sunan gwamnati.

Ta ce labaran karya da ake wallafawa sun jefa ta cikin damuwa musamman lokacin da ake rade-radin cewa shugaban kasa ya mutu da kuma lokacin da aka ce shugaban zai kara aure.

"Ban dauke shi da muhimmanci ba saboda miji na ma bai san abinda ke faruwa ba," ta ce game da rade-raden kara auren shugaban kasar.

"Dukkan mu ba mu san abinda ke faruwa ba; kawai sun fara yadda labarin ce a kafafen sada zumunta. Yanzu suna amfani da kafafen sada zumunta domin kawo karshen gwamnati.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sanatoci da ministoci da kotu ta ce su dawo da fanshon da suka karba a matsayin tsaffin gwamnoni

"Ina tunanin bai dace mu kyale mutanen da ba su kai sun kawo ba su ci zalin 'yan kasa na gari; Ban san dalilin da yasa mutanen da ya dace su dauki mataki suka yi shiru ba yayin da bata gari ke kwace kasar daga hannun mu. Ba zai yiwu ba kuma ba zamu amince da hakan ba."

Aisha ta kuma ce hadiman shugaban kasa da sauran ma'aikatan gwamnati suna watsi da muhimman abubuwan da ya dace su dauki mataki a kai kana suna mayar da hankali kan abubuwan da bai shafi shugaban kasa ba.

Ta ce, "Duk lokacin da ya dace su (hadiman shugaban kasa) su dauki mataki kan masu aikata laifuka ko su gargadi su sai su ja bakinsu suyi shiru."

"Amma idan abubuwan da ba su da muhimmanci ne mutane za su fara magana kan shugaban kasa. Misali shine abinda ya faru bayan zaben Bayelsa. Lokacin da PDP ta fito ta ce za ta dakatar da tsohon shugaba, Goodluck Jonathan kan aikata wani laifi ko wani abu mai kama da haka.

"Ban ga dalilin da zai sa fadar shugaban kasa ta fito ta ce tayi mamakin jin hakan ba. Matsalar su ne? Su 'yan PDP ne? Shin Jonathan dan jam'iyyar mu ne? Mene hadin fadar shugaban da lamarin?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164