Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa

Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa

- Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, ta kammala wata katafariyar gadar kasa wacce take da hawa guda uku

- Ana sa ran gadar zata rage mugun cunkoson da ke kan titunan babbar cibiyar kasuwancin ta yankin arewa

- Sai dai kuma, Gwamnan ya yi watsi da harkar ilimi a jihar ta yadda yake tabarbarewa a kullum

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancon gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ta dandasawa mutanen jihar wata gadar kasa mai hawa guda uku.

Gadar na nan a titin Magaji Dambatta, tsohon sha tale-talen Dangi.

Gwamnatin jihar Kano dama ta bayyana cewa, za a kammala gadar cikin rabin shekarar nan ko karshenta.

Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Asali: Facebook

A kokarin bunkasa aiyuka tare da shawo kan matsalar cunkoson motoci a jihar, gwamnatin na kokari wajen kammala aiyukan tituna gadoji da dai sauransu.

Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rashin kirkirar sabbin masarautu a Kano shi ya fi alkhairi - Sheikh Daurawa

Sai dai kash! Za a iya cewa gwamnatin jihar Kano din ta yi watsi da harkar ilimi a jihar. A halin yanzu, ilimi ya yi tabarbarewar da za a iya cewa, duk gwamnatocin da suka gabata, babu wacce ta nunawa ilimi halin ko-in-kula kamar wannan gwamnatin.

Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Asali: Facebook

Sanannen abu ne kuwa, ilimi shine gishirin zaman duniya. Ko a birnin kasuwancin na arewa, ilimi ba karamar rawa zai taka ba wajen bunkasa kasuwancin da wayar da kai.

Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Asali: Facebook

Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Kyawawan hotunan gada mai hawa 3 da Ganduje ya dandasawa Kanawa
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: