Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin jefa El-Zakzaky gidan kurkukun Kaduna

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin jefa El-Zakzaky gidan kurkukun Kaduna

Labarin da muke kawo muku da dumi-duminsa shine babbar kotun tarayya dake zaune a Kaduna ta bada umurnin dauke shugaban kungiyar mabiyar akidar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, daga ofishin hukumar DSS.

Alkalin ya bayyana cewa a mayar da Sheikh Zazzaky gidan gyara halin jihar Kaduna.

Alkaliy mai shari'a, Jastis Gideon Kudafa, ya bayyana cewa dalilin da yasa a bada wannan umurni shine domin baiwa likitoci da lauyoyin El-Zakzaky daman ganinshi lokacin da suke bukata.

Saboda haka, ya dage karan zuwa ranar 6 ga watan Febrairu, 2019 don cigaba da sauraron.

Shugaban kungiyar Shi'an na fuskantar tuhumar tayar da tarzoma, barazana da kasa, da sauran su.

Za ku tuna cewa Alkalin Gideon Kudafa ya dakatad da sauraron karar Zakzaky tun lokacin da aka nadashi Alkali a kotun zaben jihar Yobe.

A baya mun kawo muku rahoton cewa daya daga cikin iyalan shugaban kungiyar mabiya akidar Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya ce rabon da su gana da mahaifinsu tun lokacin da ya dawo jinya daga kasar Indiya.

Dan gidan Zakzaky, Badamasi Ya'akub, ya bayyana a jawabin da ya saki ranar Talata cewa basu hadu da shugabansu ba tun dawowarsa daga Indiya.

Ya sakin jawabin ne domin mayar da martani ga hukumar DSS da suka yi jawabi a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel