Tirkashi: An samu dan kamfe na 'yan mata sama da guda 100 a dakin wani saurayi

Tirkashi: An samu dan kamfe na 'yan mata sama da guda 100 a dakin wani saurayi

- Mutanen kauyen Hirumbi a kasar Kenya sun kusa bankawa wani barawon dan kamfan mata wuta

- Matan yankin sun koka da yadda ake sace musu dan kamfai matukar sun wanke sun shanya

- Barawon mai suna Mukoshi ya ce, tsananin fatara da talauci ne yasa ya fada harkar satar dan kamfan

An kusa bankawa wani mutum mai shekaru 36 wuta a kauyen Hirumbi na Larambi da ke Kakamega a kasar Kenya.

A ranar Lahadi ne aka cafke mutumin da dan kamfai na mata guda 100 da ya sato.

A yayin wani bincike da mazauna yankin ke yi, an kama wanda ake zargin mai suna Mukoshi Chipukosia, sanye da dan kamfan guda biyu cikin wadanda ya sato na mata.

Shugaban kungiyar Nyumba Kumi, Eric Anyanjira, ya sanar da K24 yadda suka fara zargin Mukoshi, saboda a duk lokacin da ya cire kaya za a ganshi ne da kayan ciki na mata. An ganshi ba sau daya ko biyu ba a rafi in yaje wanka.

A ranar Lahadi ne aka zargi Mukoshi da satar wasu kayan ciki na mata daga makabtansu. Karnuka ne suka tona mishi asiri ta hanyar haushinsu.

"Lokacin da naje dubawa, na ga ya kwaso dan kamfan mata ya zuba a aljihu," in ji wata fusatacciyar mata.

KU KARANTA: Babban Shehi yayi kaca-kaca da jarumar fim da tace zata sha tabar wiwi da Al-Qur'ani

"Akwai wata mata a makwabta da kullum take koken ana sace mata kayan ciki. Idan mata suka yi wanka, suka bar dan kamfai a bayi, ya kan bi ya sace," in ji wata mata.

"Mun gaji da wannan dabi'ar! Me yake yi dasu? Dan kamfan mata kadai yake sata, banda na maza. Yana barinmu cikin tunanin me wannan barawon ke yi dasu?" Inji wata mata daban.

"A lokaci mai tsawo da muka sani, ana satar shanu, awaki da kaji a wannan yankin. Amma yanzu, sai muka samu barawon da ya kware wajen satar kayan mata. Komai sata akeyi," cewar wani mutum mazaunin yankin.

An tirsasa Mukoshi da ya zubar da kayan ciki na matan da ya sato kuma ya yi alkawarin ba zai kara satar dan kamfan mata ba.

Wanda ake zargin yace fatara da tsananin talauci ne yasa yake wannan satar.

"Banda kudin siyan dan kamfan maza. A don haka ne banda wani abu da ya wuce satar na matan," cewar Mukoshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel