Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Osun

Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Osun

Hankula sun tashi a kauyen Iyere dake karamar hukumar Atakumosa West ta jihar Osun a ranar Litinin inda akalla mutane uku suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa.

Duk da cewa har yanzu ba'a san abinda ya haddasa rikicin ba, majiyoyi da dama sun bayyanawa jaridar Tribune cewa an samu sabani ne tsakanin wani bahaushe da bafillace sai wani bayarabe ya shiga rabasu.

Daga raba fada sai aka kai mai sara aka kashe shi.

Kawai sai Yarabawan unguwar suka farwa masu fadan kuma suka hallakasu har lahira.

Sakamakon haka rikici ya barke tsakanin kabiluna garin Itagunmodi da Igila.

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda jihar Osuna, ASP Mustapha Katayeyanjue, ya tabbatar da faruwan haka amma yace mutum daya kadai aka kashe.

Yace: "Wani 'Baguga' ya kashe wani matashi mau suna, Tope Kayode, kan dalilin da bamu tabbatar ba. Sakamakon haka aka kona shagunan mutane a garin."

"An ajiya gawarsa a dakin ajiye gawawwakin asibitin Westley Guild domin gudanar da bincike kan gawan kafin bincike kan ainihin lamarin."

"An baza jami'an tsaro don kwantar da kuran da kuma damke wadanda suka haddasa rikicin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel