Jerin sunayen kwamishinoni 19 da gwamnan Zamfara ya aika ma majalisar dokokin jahar

Jerin sunayen kwamishinoni 19 da gwamnan Zamfara ya aika ma majalisar dokokin jahar

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya aika ma majalisar dokokin jahar Zamfara sunayen mutane 19 da yake muradin nadasu mukamin kwamishinoni a gwamnatinsa, domin ta tantancesu.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito kaakakin majalisar dokokin jahar, Alhaji Nasiru Magarya ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Talata, 3 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Rikicin Yan-Uba: Dubun barawon daya sace kanwarsa yar shekara 6 a Katsina ta cika

A jawabinsa, Kaakaki Nasiru Magarya ya bayyana cewa baya ga sunayen kwamishinoni 19 da gwamnan ya aika ma majalisar, akwai kuma sunayen manyan mashawarta na musamman guda 28 da gwamnan ya aika musu.

Wasu daga cikin sunayen da wasikar gwamnan ke dauke dasu sun hada da: Alhaji Sulaiman Tunau, Alhaji Aminu Sulaiman, Malam Abdulkadir Gora, Malam Jinaidu Muhammad, Malam Muhammad Maiturare, Zainab Gummi, Jamilu Aliyu, Dr Nura Isah da Rabiu Garba.

Sauran sun hada da Malam Sufyanu Yuguda, Malam Ibrahim Magayaki, Mr Yahaya Gora, Yahaya Kanoma, Sheik Tukur Jangebe, Malam Ibrahim Mayana, Abubakar Tsafe, Nura Zarumi, Bilyaminu Shinkafi da Abubakar Muhammad.

Daga karshe kaakakin majalisan ya bayyana cewa zasu sanya ranakun da zasu gudanar da tantancewa ga sunayen da gwamnan ya aika musu.

A wani labarin kuma, Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara ya yi addu’ar Allah Ya saukar da fushinsa a kan duk masu cin mutuncin Al-Qur’ani a jahar Zamfara, sa’annan ya yi kira ga al’ummar jahar Zamfara dasu cigaba da rokon Allah a kan wannan matsala.

Matawalle ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 2 ga watan Disamba yayin bude taron gasar Al-Qur’ani mai girma na shekarar 2019 daya gudana a garin Gusau inda yace addu’an ya zama wajibi saboda masu aikata laifin nan suna tafka mummunan badala wanda ka iya janyo masifa a jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel