Amfanin tafiye-tafiyen shugaba Buhari ga 'yan Najeriya - Hadiminsa

Amfanin tafiye-tafiyen shugaba Buhari ga 'yan Najeriya - Hadiminsa

Ajuri Nagelale, babban mataimakin shugaban kasa Muhammadu Buhari a bangaren mu'amala da mutane, yace ‘yan Najeriya na matukar amfana da tafiye-tafiyen shugaba Buhari.

Ngelale ya sanar da hakan ne a tattaunawar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja, yayin bayyana amfanin tafiye-tafiyen shugaban kasar.

Ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban da sauran kasashe ke kallo da nagartaccen mutum. “Wadannan tafiye-tafiyen na da matukar amfani. Muna amfana ne da su sakamakon nagarta da yaki da rashawar da kasashen duniya suka san shi dasu. A don haka ne ‘yan Najeriya suke morewa daga hakan.” In ji shi.

Ngelale ya bayyana cewa, akwai yuwuwar ‘yan Najeriya su more daga tafiye-tafiyen shugaban kasar ta hanyar gina tattalin arziki mai matukar karfi.

DUBA WANNAN: Masu zanga - zanga sun rufe hanyara Kaduna zuwa Abuja a kan sakamakon zaben kananan hukumomi

“Tafiyar shugaban kasar zuwa kasar Rasha da kuma masarautar Saudi Arabia duk don amfanin kasar nan ne. Na sanar da hakan ne saboda irin abubuwan arzikin da kasar nan ta samu sakamakon wadannan tafiye-tafiyen.

“Mun yi matukar murna da ziyara da ya kai kasar Rasha sakamakon yarjejeniya kala-kala da kasashen biyu suka saka hannu,” in ji shi.

Hadimin shugaban kasar yace, kadan daga cikin ma’aikatu da bangarorin da zasu mori wannan tafiyar sun hada da bangaren hako ma’adanai da habakasu, sufuri, tsaro da sauransu.

Za a farfado da kamfanin sarrafa karafuna na Ajaokuta ta yarjejeniyar da kasar Rasha, Najeriya da bankin Afrexim suka sa hannu.

Kamar yadda ya ce, wannan zai sa bangaren karafuna na Najeriya ya farfado kuma a daina shigo da karafuna kasar nan. Ta hakan kuma za a samar da aiyuka ga matasa tare da fatattakar talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel