Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi sabbin shugabannin hukumar jin dadin alhazai NAHCON

Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi sabbin shugabannin hukumar jin dadin alhazai NAHCON

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sunan sabon shugaba da mambobin hukumar jin dadin lahazai NAHCON majalisar dattawa domin tabbatar da su.

A wasikar da PRNigeria ta samu, Buhari ya bayyana cewa: "Bisa ga sashe na 3 (2) na dokar kafa hukumar jin dadin alhazai 2006, ina farin cikin gabatar maka da wadannan sunayen na matsayin shugaba da mambobin hukumar jin dadin alhazai."

Sabon shugaban shine Zikrullah (Sikiru) Olakunle Hassan daga jihar Osun.

Sauran manyan kwamishanonin sune Abdullahi Magaji Hardawa (Bauchi,), Nura Hassan Yakasai (Kano, ) da Sheikh Momoh Suleman Imonikhe,(Edo).

DUBA NAN Rufe boda: Mun gano daruruwan gidajen mai a Magama Jibiya - FG

Mambobin wucin gadi sun hada da Halimat Jibril (Jihar Niger), Abbas Jato, (Jihar Borno), Garba Umar, (jihar Sokoto); Ibrahim Ogbonnah Amah, (jihar Ebonyi), Sadiq Oniyesaneyene Musa, (jihar Delta) da Mrs. Akintunde Basirat Olayinka, (jihar Ogun).

Wakilan ma'aikatu da hukumomin gwamnatin sune Shehu Dogo, ma'aikatar sufurin sama, Nura Abba Rimi, ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Rabi Bello Isa, ma'aikatar kudi, Zainab Ujudud Sheriff, ma'aikatar lafiya, Aminu Bako Yarima, hukumar shiga da ficen Najeriya da Ibrahim Ishaq Nuhu daga babban bankin Najeriya CBN.

PRNigeria ta samu rahoton cewa za'a tura sunayen wakilan kungiyar Jamaatul Nasril Islam da majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci NSCIA idan aka kammala shawara akai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel