Rufe boda: Mun gano daruruwan gidajen mai a Magama Jibiya - FG

Rufe boda: Mun gano daruruwan gidajen mai a Magama Jibiya - FG

Gwamnatin tarayyya ta bayyana cewa an gani daruruwan gidajen mai da aka gina musamman don fasa kwabrin man fetur a iyakan Najeriya da Nijar dake Magama Jibiya, jihar Katsina.

Gwamnati ta bayyana cewa fasa kwabrin man fetur, bakin haure, shigo da makamai, fasa kwabrin shinkada daga iyakokin Najeriya da Kotono da Nijar ne manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana hakan ne yayinda tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyara iyakan Najeriya da Nijar, Magama Jibia.

Ya ce wadannan gidajen man basu sayar da mai da rana sa cikin dare. Hakazalikabasu sayarwa jama'a sai tankoki.

DUBA NAN Bayan rikice-rikicen kotu, Jerin Sanatoci mata 8 dake majalisar dattawan Najeriya

A cikin tawagar akwai karamin ministan kasafin kudi, Clement Agba; karamar ministar kasuwanci, Maryam Katagum da manyan jami'an hukumar shiga da fice da kuma Kwastam.

Ministan ya ce tun lokacin da aka rufe iyakokin Najeriya, an samu karin kudin haraji na kimanin nashi 30%.

Yace: "An gina wadannan gidaje man ne kawai don fasa kwabrin man fetur. Ba su sayar da man da aka kai musu ga jama'a. Hakazalika yawancinsu na yan bakin haure ne."

"Rufe iyakokin ya rage shigowar makamai da harsasai saboda yan bindiga da yan ta'adda basu samun siyan, shi yasa aka smaun sauki sace-sacen shanaye, garkuwa da mutane, barandanci da suka addabi yankin Arewa maso yamma."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel