Dalilin da yasa muke rike kudin albashin masu N-Power - Gwamnatin tarayya

Dalilin da yasa muke rike kudin albashin masu N-Power - Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta yi bayanin dalilin da yasa har yanzu ba'a biya ma'aikatan N-Power a fadin kasa kudin albashinsu ba na watanni biyu.

Shirin N-Power wani shiri ne da gwamnatin Buhari ta shirya domin rage yawan matasa maras aikin yi a fadin tarayya.

A cewar ministan walwal da jin dadin al'ummar, Hajiya Sadiya Farouq, an samu jinkiri ne saboda ba'a kammala mika ragamar aiki daga ofishin mataimakin shugaban kasa zuwa sabuwar ma'aikatar ba.

A wa'adin Buhari na farko, ofishin ta kasance karkashin mataimakin shugaban kasa kafin Buhari ya kwace ya baiwa Hajiya Sadiya Farouq.

Hakazalika ta bayyana cewa wani dalilin shine har yanzu ba'a san yadda za'a yi da wadanda ya kamata a sallama ba duk da cewa wa'adinsu ya kare.

Ta bada tabbacin cewa za'a biya dukkan kudaden jama'a muddin aka kammala abubuwan da akeyi kuma a cigaba da shirye-shiryen.

Tace: "Har yanzu ba'a sallami ma'aikatan N-Power da aka dauka a shekarar 2016 ba watanni 16 bayan karewa wa'adinsu; ya kamata ace an yayesu zuwa wani aikin."

Ma'aikatar da tabbatarwa matasan cewa za'a biyasu basussukan muddin aka kammala mika ragamar mulki."

Ta kara da cewa babu gaskiya cikin jita-jitan cewa za'a soke shirin

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel