Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa dan majalisar wakilai, Jafaru Iliyasu, rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa dan majalisar wakilai, Jafaru Iliyasu, rasuwa

Innan lillahi wa inna ilaihi raji'un

Wani dan majalisar wakilan tarayya daga jihar Neja, Jafaru Iliyasu Auna, ya rigamu gidan gaskiya.

Jafaru Auna ya rasu ne da safiyar yau Litinin bayan gajeruwar jinya da yayi a babbar asibitin Maitama, dake birnin tarayya Abuja.

Ya kasance mamban majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rijau/Magama.

Tabbatar da labarin, wani dan majalisar jihar Neja Saidu Abdullahi ya bayyana cewa marigayin ya dawo daga jihar Legas ranar Lahadi amma ya rasu da safiyar Litinin.

Hakazalika mataimakin bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Sabi Abdullahi, shima dan jihar Neja ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel